You are currently viewing ZIYARAR ALLAH

ZIYARAR ALLAH

Musa kuwa ya dauki kasusuwan Yusufu tare da shi, gama ya rantsadda yayan Israila da karfi chewa, Hakika Allah za ya Ziyarce Ku: Sai ku tafi da kasusuwana daga nan tare da ku. Fitowa 13:19

Tattaunawan mu zai kasanche a kan anabcin Yusufu cewa “Hakika Allah za ya ziyarce ku.” Cikin bauta a Masar, Allah ya shirya ya ziyarce mutanensa. Wannan ya nuna jinkan Allah. A kasar Masar, Israila bata da baki ko wakili a fadar  Firauna, an kuwa shirya za’a hallakasda su amma shirin Allah dominsu dabam ne. Allah za ya ziyarce su da dalili. Wannan domin ya fara madauwamiyyar shirinsa da Ibraniyawa ne wannan ya sha gaban shirin Fir’auna.

Tambaya na farko da za mu yi wa kanmu ita ce, menene shirin Allah domina? Rashin sanin shirin Allah a kanmu zaya hana mu san lokacin ziyaransa. Yana yiwuwa akwai abubuwa masu kyau da Allah ya shirya maka amma, mafi muhimanci, ita ce  ceton ranka. Watau fansar ranka ne daga madauwamiyyar lallacewa a hades. Ranka yana tsananin bukatar ceto domin zunubi ya sa maka tabo. Rayuwar zunubi ya raba ka daga kaunar Allah da ziyararsa. Mai zunubi ba ya hangon gaba. Ba ya iya sanin wahalarsa a hades, baya  ma sanin jinkar Allah da dadin da ke a mazaunin mai iko. Don haka ya zaba nasa hanya.

Yadda Israila tana cikin tallauci da bauta a Masar, mai zunubi ya tallauce a ruhu, yana bakin bautar zunubi. Bawan zunubi ne, yana bukatar ziyarar Allah bisa ga anabcin Yusufu. Hakika Allah za ya ziyarce ku. Allah yana da babbar niyar yancinka. Kalmar “hakika” yana cewa lallai, babu fasawa, tabbatace wannan ya nuna cewa ziyarar Allah tabbas ne idan mun ba wa Allah zarafi, ko wuri a rayukanmu. Komi zurfin fadiwarka cikin zunubi, ya yiwu kana tsakiyar anishuwa da zunubi, hakika Allah za ya ziyarce ka a wurin domin ya fanshe ka daga ciki.

Da a ce akwai wani mutumin Israila da ya ki fita daga masar lokacin cetonsu, da mutumin ya hallaka a karkashin mugun hannun Firauna. Rayuwa cikin zunubi yana kai ga madauwamiyyar hallaka.

Yanzu fa in ji Ubangiji mai runduna: ku lura da al’ammuranku. Haggai 1:5 Yaya ne hanyoyinka sun kasance gaban ubangiji? Lura da shi ko na kin tuba da rabuwa da zunubi gaba daya? Lura da shi . Tuna  idan ka rasa ranka har abada. Amma Allah wanda yana cike da jinkai, domin yawan kaunarsa daya kaunace mu yana shirye ya ziyarce ka. Kada ka ki jinkansa amma ka yarda. Akwai warewa idan ka ki Ubangijinmu kuma za ka lallace begenka na madauwamiyar safe domin yaudarar zunubi da abubuwa da yake bayarwa. Zo ka sami warkewa, mika kanka ga yesu. Ka yi lissafin tamanin? Babban rana tana zuwa da za a raba masu zunubi daga Allah. Ka shirya domin ranar sharia? Kowane ziyara daga Allah yana kawo sakewa a rayuwar mutane da ya ziyarta. Alama na farko da ya nuna Allah ya ziyarce mai zunubi shine sakewa daga rayuwar zunubi zuwa tsarki. Idan kowane mutum yana cikin kristi. Watau ya fita daga cikin zunubi ya zama sabon halitta, tsohon rayuwan zunubi ya shude domin sabon shugaba, maigida da mai mulki ya dauki mazauninsa.

HAKIKA ALLAH ZA YA ZIYARCE KA

Bayan  shekaru fiye da Dari hudu, anabcin Yusufu ya cika a kan yayan Israila. Allah ya ziyarce su, ceto ya zo masu. Wannan shine lokacin ziyararka daga Allah. Zunubi zaya kare a rayuwanka idan ka karbe shi, ka tuba ka kuma yi addu’a domin gafara. Ubangiji Allah, Ina rokon jinkai da alherin ka a Rai na. Na zo gareka cikin tuban gaskiya. Ka Yi Mani gafara ka wanke ni da jinin Yesus Mai daraja kuma ka rubuta suna na cikin littafin Rai cikin sunan Yesu.

Cin gaba a ruhanniya ita ce damuwanmu.